Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Ma'aikata Masu Wayar da Kawunan Jama'a Kan Cutar Ebola a Kasar Guinea


Sanarwa kan ebola a Guinea
Sanarwa kan ebola a Guinea

Kwana biyu bayan sun bace an gano gawar ma'aikatan kiwon lafiya masu wayar da kawunan jama'a kan cutar ebola a wani kauye dake kasar Guinea, kasar da cutar ta yiwa katutu

A kudu maso gabashin kasar Guinea an samu gawar wani dake aiki da masu wayar da kawunan jama’a akan cutar ebola jiya Alhamis.

Ganowar gawar ta zo ne yayinda hukumar tsaro ta MDD ta yi shelar cewa cutar ebola tana yiwa zaman lafiya da tsaron duniya barzana.

To sai dai kuma jami’an kasar Guinea sun sanarda cewa wasu mazauna kauye sun kashe ma’aikatan kiwon lafiya bakwai da ‘yan jarida a kudu maso gabashin garin Wome bayan an kwashi kwana biyu ana nemansu.

Shugabannin duniya da MDD sun nuna damuwa da yadda cutar ke yaduwa. Kimanin kusan mutane 2,600 suka mutu tun da annobar ta barke a kasashen Guinea, Liberia da Saliyo.

A wani taron gaggawa da hukumar tsaro ta MDD tayi mambobinta baki daya suka dauki kudurin kiran ksashen dake cikin majalisar suka kara taimakon da suke bayarwa domin shawo kan annobar.

Ta kuma bukaci kasashe su inganta hanyar sadarwa da jama’a domin a kawar da rudani da fargaban ba gaira ba dalili akan kayar cutar.

Babban Sakataren MDD Ban Ki-moon ya sanarda kafa wata kungiyar gaggawa ta musamman ta majalisar akan tunkarar cutar ebola.

Sabili da haka MDD zata aika da manzo na musamman da zai zauna a yankin da cutar tayi kamari wanda

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG