Lamarin dai ya faru ne a kauyen Yar Tashar Sahabi dake Gundumar Dansadau a Karamar hukumar Mulkin Maru a Jihar Zamfara, kwanaki kadan bayan da wata nakiyar ta tashi da wata motar dakon kaya akan gadar shiga garin 'Yar Galadima duka a wannan yankin dake tazarar kilomita 12 zuwa garin 'Yar Tashar Sahabi.
A hirar shi da Muryar Amurka, wani mazaunin garin na Yar Tashar Sahabi ya ce sun samu labarin fitowar 'yan bindigar akan babura suka dauki mataki ba tare da sanin cewa, sun haka nakiya akan hanyar ba.
“Tun da misalin karfe daya na dare aka sanar da mu cewa, sun fito, kuma mun hango fitilun mashinan su, ashe sun fara dasa nakiyar ne. Da jami'an tsaro sun zo kawo mana dauki da abun ya tashi da su, Allah ya tsare jami'an tsaro ba su bi ta nan ba shi ya sa direban Gof ya taka.”
Yace motar dai tayi kaca-kaca, kuma mutun biyu sun mutu, wasu sun samu rauni yayin da wasu kuma suka fita ba tare da samun wata matsala ba.
Shima wani da ya ganewa idon sa yadda abun ya faru, yace lamarin na da ban tsoro duk da cewa jami’an tsaron da ke yankin suna kai masu dauki cikin lokaci, akwai bukatar samar masu da karin kayan aiki da basu kwarin guiwa.
Da yake bada tabbacin faruwar lamarin, Lt Col Abubakar Abdullahi wanda ke magana da yawun rundunar tsaro ta hadin guiwa don yakar ayukkan ta'addanci a yankin Arewa Maso yammancin Nigeria da ake kira Operation Fansar Yamma, yace, jami'an tsaro na nan a bakin daga, kuma ba za su ja da baya ba ko suyi kasa a guiwa har sai sun tabbatar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
“Mun tura dakarun mu kuma sun je wurin tare da kwararru akan kwance nakiya don kara inganta tsaro a yankin, kuma muna nan a bakin daga ba za mu ja da baya ba. Muna rokon al'umma da su ci gaba da bamu hadin kai don ganin mun samu nasara.”
Ayukkan 'yan bindiga a Jihar Zamfara dai yayi sanadiyyar mutuwa ko jikkata dubban mutane tare da raba wasu da dama da muhallan su da kuma kawo nakasu ga sha’anin tattalin arzikin Jihar.
Saurari cikakken rahoton Abdulrazak Bello:
Your browser doesn’t support HTML5