Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Jami’an Rundunar Sa-Kai 23 A Wasu Hare Hare A Jihar Borno


Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

Akalla jami'an rundunar sa-kai ta Civilian JTF ashirin da uku aka kashe a Najeriya a ranar Asabar a wasu hare-hare biyu da mayaka da ‘yan bindiga masu satar mutane suka kai a arewacin kasar.

A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda tashin hankalin ‘yan boko haram ya fi kamari, wasu da ake kyautata zato mayakan kungiyar ISWAP ne sun yi amfani da nakiya wajen tarwatsa wata mota da ke dauke da tawagar jami’an sa-kai da ake kira Civilian JTF a takaice ko CJTF, a cewar wani shugaban karamar hukuma.

An kafa rundunar ta CJTF ne a shekarar 2013 domin kare al’ummomin yankin arewa maso gabas da kuma taimaka wa sojoji wajen yakar mayakan Boko Haram, da kuma 'yan ISWAP da suka balle daga baya. An fadada rundunar zuwa wasu jihohin arewacin Najeriya da ke fama da kungiyoyin masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Civilian JTF, Maiduguri, Nigeria, December 2013
Civilian JTF, Maiduguri, Nigeria, December 2013

Tijjanima Umar, shugaban rundunar CJTF a yankin Gamboru Ngala da ke kusa da kan iyaka da Kamaru, ya ce tawagar jami’ansa na kan hanyar zuwa Maiduguri babban birnin jihar Borno, sai motarsu ta taka nakiya.

“Yayin da nakiyar ta tashi, tara daga cikinsu sun mutu nan take, wasu mutane biyu kuma sun jikkata sosai kuma an kai su asibiti ba tare da bata lokaci ba,” abinda Umar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho kenan.

Nan take dai Rundunar sojan Najeriya ba ta maida martani ba akan aukuwar lamarin.

Duk da cewa jami'an tsaron Najeriya sun karya laggon su, kungiyoyin Boko Haram da ISWAP na ci gaba da kai munanan hare-hare kan farar hula da sojoji.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG