A wajen wani taron gangami da Nakasassu suka gudanar sun yi addu’o’I ne na musamman game da halin da suke ciki bayan da gwamnatin jihar ta yi watsi da su. Gwamnatin jihar dai ta musanta wannan zargi.
Sakataren kungiyar guragun jihar Adamawa, Mr. George Pauro Numan, yana daya daga cikin shugabannin nakasassun da suka gudanar da taro, inda yace sunyi taron ne domin su yi addu’a su roki Allah, kan ya taba zuciyar shuwagabanni don su ci gaba da tunawa da nakasassu.
Shima Isah Abubakar daya daga cikin shugabannin nakasassu, yace yau fiye da watanni 30 kenan ba a biya su albashinsu na Naira Dubu uku da ake basu kowanne wata.
Sai dai kuma a martanin da gwamnatin jihar Adamawa ta mayar kan wannan batu, ta musunta zargin cewa tana nunawa nakasassun jihar wariya, ta bakin kwamishinan yada labaran jihar Kwamarad Ahmed Sajo, ta danganta batun ne da rashin kudin da yace gwamnatin jihar na fama da shi a yanzu.
Domin karin bayani saurari rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5