Nakasassu Sun Shiga Halin Kakanikayi A Jihar Taraba

Wasu nakasassu

A jihar Taraba nakasassu sun shiga wani halin kakanikayi inda suke shiga sako sako domin neman abun da zasu ci a wannan watan Ramadan suna bara da a basu na Annabi

Yasu nakasassun suna tafiya da 'yan jagora domin neman inda ake raba kayan masarufi na azumi.

Wannan lamarin na zuwa ne yayinda ma'aikata ke kukan rashin albashi kana 'yan kasuwa ke cewa babu ciniki sakamakon matsalar tattalin arziki da ake fama dashi a yanzu. Matsalar rashin kudi ta shafi harkokin yau da kullum da kuma walwalar jama'a.

Wata nakasasshiya tace suna rayuwa cikin kunci. Haka ma wani yace halin da suke ciki bashi da kyau. Yace akwai wasu da basu da abun da zasu ci gaba daya kuma ga azumi.

Nakasassun dai sun bukaci gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su taimaka masu. Suna rokon gwamnati ta dinga tunawa dasu.

Kwamred Sadiq Jalingo shugaban hadakar kungiyoyin nakasassun jihar ya bayyana bacin ransa ne dangane da abun da aka yi masu bana. Yace nakasassu da aka yi masu rajista sun fi dubu biyar amma sai aka basu buhun dawa takwas da na sukari uku. Yace ta yaya zasu rabasu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Nakasassu Sun Shiga Halin Kakanikayi A Jihar Taraba - 3' 22"