KUMASI, GHANA - Matakin soke dokar karban harajin ya sanya masu fama da nakasa cikin mawuyacin hali saboda su suke da alhakin karban wannan harajin titi na Toll levy.
Wani saurayi Mallam Abdul Rashad mai fama da nakasa da yake karban harajin titi a Tema a jihar Accra ya fada wa Muryar Amurka cewa tun lokacinda gwamnati ta soke karban harajin bayada sana'ar yi kuma hakan na tasiri akan neman ilimin ‘ya’yansa.
Shugaban kungiyar masu fama da nakasa a jihar Ashanti Mr. Steven Gyan ya ce soke wannan shirin ya janyo matsala sosai ga nakasassu saboda ‘ya’yan wasu sun daina zuwa makaranta kazalika wasu sun rasa rayukansu.
Domin sanin ko wane mataki gwamnati ke dauka akan masu fama da nakasa a kasar, mun tuntubi shugaban kungiyar Nasara mai fafutukan nemawa jam’iyyan NPP mai mulki a Ghana farin jini amatsugunin musulmin Ghana, wato National Nasara Cordintor Abdul Aziz Haruna Futa, ya ce gwamnatin jam’iyyan NPP ce kadai ta maida hankali gurin taimakon masu fama da nakasa ciki harda nada gurgu amatsayin ministan jihar Oti ta kasar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adam:
Your browser doesn’t support HTML5