Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Ghana Sun Yi Zanga-Zanga A Kan Tsadar Rayuwa


Zanga-zanga
Zanga-zanga

Jami'an 'yan sandan Ghana sun yi amfani da barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar da kungiyar fafutuka ta ‘Arise Ghana’ ta shirya, domin bayyana korafinsu a kan tabarbarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa da al’ummar Ghana ke fuskanta.

Wannan na zuwa ne biyo bayan arangama da aka samu tsakaninsu a babban shatale-talen Kwame Nkrumah da ke birnin Accra.

Zanga-zangar da aka fara cikin lumana kafin daga baya ta rikide ta koma tashin hankali bayan tattaunawa da aka yi tsakanin ‘yan sandan da shugabannin ‘yan zanga-zangar domin samun maslaha a kan hanyar da ‘yan zanga-zangar za su bi, zuwa inda za su mika korafinsu.

Zanga-zanga
Zanga-zanga

Bayan tattaunawansu da ‘yan sanda sai daya daga cikin jagororin zanga-zangar, Bernerd Monarh ya zo ya yi wa jama’a jawabi inda ya bayyana rashin amincewa da matsayin 'yan sandan sai dai ya yi kira ga magoya baya da kada su yi tashin hankali.

Zanga-zanga
Zanga-zanga

Ba da jimawa ba da wannan jawabi na sa, sai ‘yan sanda da suka kange manyan tagwayen hanyoyin Ring road suka fara jefa hayaki mai sa hawaye bayan da ‘yan zanga-zangan suka fara jifarsu, domin sun hana su bin hanyar zuwa fadar gwamnati; hanyar da kotu ta yanke hukuncin kada su bi, gabanin a kaddamar da zanga-zangar.

Zanga-zanga
Zanga-zanga

A hira da wasu da suka halarci wajen, sun nuna cewa ‘yan sanda ba su yi musu adalci ba, kuma ba za su ja da baya ba.

Hukumar ‘yan sandan Ghana, a wani jawabi da ta fitar ga manema labarai da sa hannun darektar hulda da jama’a, Grace Ansah Akrofi ta tabbatar da amfani da barkonon tsohuwar da kuma mesar ruwa domin tarwatsa masu zanga-zangar bayan awkuwar hargitsin.

Jawabin ya kara da cewa, “Hargitsin ya faru ne a sanadiyar kin bin hukuncin da kotu ta yake cewa masu zanga-zangar ‘Arise Ghana’ su fara jerin gwanonsu daga inda suke zuwa dandalin ‘yanci dake cikin Accra. Amma, sai suka ce su za su bi ta wata hanyar da za ta kai su ga fadar shugaban kasa, .

Hukumar tace, ‘yan sanda 12 sun ji rauni kuma an kai su asibitin ‘yan sanda domin jinya.

Su ma masu fafutar Arise Ghana, sun shirya taron manema labarai domin su bayyan korafinsu a kan abinda ya faru.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

XS
SM
MD
LG