NAKASA BA KASAWA BA: Wani Mai Nakasa Da Ya Dage Neman Ilimi Don Ya Zama Lauya, Kashi Na Uku - Agusta 30, 2023

Souley Mummuni Barma

A shirin na wannan makon, mun yi ban kwana ne da AbdurRahman Yusuf, lauya mai fafutikar kare hakkin takwarorinsa Nakasassu a kasar Ghana.

Jami’I a ma’aikatar jin dadin rayuwar al’umma bakon shirin abin misali ne ga masu bukata ta musamman ganin yadda ya dage da neman ilimin zamani har ya cimma burinsa na zama masanin doka.

Illolin bara a wajen Nakasassu musamman ga wadanda suka mayar da ita sana’a da matsalolin da ke tattare da tsarin biyan kudaden tallafin masu bukata ta musamman a Ghana na daga cikin batutuwan da zamu karkare hirar da ta hada shi da wakilin sashen hausa a Accra Idriss Abdallah Bako.

Saurari shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

SHIRIN NAKASA