NAKASA BA KASAWA BA: ‘Kwazon Wani Bakanike Da Ya Rasa Idanunsa Bayan Rashin Lafiya, Yuli 13, 2023

Souley Mummuni Barma

NIAMEY, NIGER - A shirin Nakasa Ba Kasawa Ba na wannan makon mun samu bakuncin Murtala Abdullahi Shu’aibu, wani bakanike haifaffen jihar Kano mazaunin babban birnin tarayyar Najeriya Abuja wanda kaddarar rayuwa ta yi sanadin makancewarsa.

Malam Shu’aibu ya bayyana cewa , shekaru sama da 20 kenan da ya daina gani bayan fama da rashin lafiya, amma kuma hakan bai katse masa hamzari yin sana’arsa ba, ballantana tunanin bin wata hanyar kaskanci.

Saurari cikakken shirin da Souley Moumouni Barma ya gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

NAKASA BA KASAWA BA: ‘Kwazon Wani Bakanike Da Ya Rasa Idanunsa Bayan Rashin Lafiya, Yuli 13, 2023.mp3