Hukumar kwallon kafa ta Najeriya,zata fuskanci fushin hukumar kwallon kafa ta duniya watau (FIFA) biyo bayan mutuwar mutane biyar a harabar filin wasan kwallon kafa na Godswill Akpabio dake Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.
Hukumar FIFA dai na zargin hukumar kwallon kafa na Najeriya ne a bisa zargin mutawar mutane biyar inda wasu kuma da dama sun samu raunuka a lokacin da kungiyar kwallon kafa na Najeriya, ta kara da kungiyar kwallon kafa ta kasar Zambia a gasar neman gurbin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya wanda aka buga ranar asabar din ta da gabata.
Alamarin ya afku ne a lokacvin da jama’a ke kokarin shiga filin wasan kwallon kafar domin domin kallon wasan najeriuya da kasar Zambia.
A wasan baya da Najeriya ta buga da kasar Kamaru, zai da hukumar FIFA, ta ci tarar Najeriya, fiye da Naira miliyan goma sha daya sakamakon shiga filin wasa da ‘yan kallo suka yi a lokacin wasa tsakanin Najeriya da kasar Kamaru a wsasan neman gurbin shiga gasar neman cin kofin kwallon kafa na duniya.