Shahararen dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa na Kasar Gabon mai taka leda a kungiyar Borussia Dortmund, mai suna Emerick Aubameyang, yace baya tunanin zai sake buga Bundesliga, na kasar Jamus, bayan an kammala wasannin wannan shekara ta 2017/18.
Emerick mai shekaru 28, a duniya haifaffen kasar Faransa ne amma iyayensa ‘yan kasar Gabon ne a nahiyar Afirka.
Kafin ya fara bugawa kasar Gabon sai da ya bugawa kungiyar ‘yan kasa da shekaru 21 na kasar Faransa, danwasan wanda ya buga wasanni a kungiyoyin kwallon kafa daban daban a duniya, ya dawo kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, a shekara ta 2013 daga tsohowar kungiyarsa ta Saint Etienne, na kasar Faransa,
A yanzu haka dan wasan ya fafata wasannin har guda 135, a kungiyar Borussia Dortmund, inda ya samu nasarar zurara kwallaye guda 93, a raga a wasanni daban daban da ya bugawa kungiyar.
Kafin rufe hada hadar saye da sayarda ‘yan wasan kwallon kafa na na bana kungiyoyi da dama irin su Manchester City, na kasar Ingila da Real Madrid, na kasar Spain, sun nuna sha'awarsu akan dan wasan na Borussia Dortmund.
Facebook Forum