Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yanke shawarar samar da hasken wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana da iska, duba da yadda tsagerun Niger Delta ke ci gaba da fasa bututun Mai a kasar, wanda hakan ke shafar hanyoyin samar da wutar lantarki.
WASHINGTON, DC —
Barista Waziri Bintube, na hukumar sayar da makamashi ta Najeriya, NBET a takaice, yace dalilin fara farfasa bututun Mai ne yasa suka yi tunanin neman wata sabuwar hanya. Yanzu haka dai an yi yarjejeniya da wasu kamfanoni har 14, guda 12 sun fito ne daga kasashen waje wadanda zasu gudanar da wannan aikin.
Ana sa ran dai cikin wata shida za a kammala wannan aikin, ta yadda al’umma zasu fara ganin banbanci musamman wajen wutar lantarki.
A cewar wani ‘dan Najeriya Sabo Imam Gashua, yana murna da maraba lale da kuma goyon baya ga wannan mataki da gwamnati ta kawo na samar da wutar lantarki da ta hanya ta zamani wato ta amfani da hasken rana.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5