Najeriya Zata Biya Dala Dubu Biyar Ga Hukumar CAF

CAF

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta nemi Najeriya da ta biya tarar kudi har dalar Amurka dala dubu biyar $5000, a dalilin rashin ‘da’a wani ‘dan Najeriya yayi alokacin da kasar ke wasan neman shiga wasannin gasar cin kofin nahiyar Afirka mai zuwa na shekara ta 2017.

Najeriya da Chadi sun buga ne filin wasan Ahmadu Bello dake jihar Kaduna, ranar Litinin 13 ga watan Yuli wannan shekarar, inda Super Eagles suka lashe wasan da ci biyu da babu 2-0.

Hukumar kwallon ta kafe wannan sanarwar ne a shafinta na yanar gizo. Sun dai bayyana cewa jami’an ‘da’a na hukumar sun cimma matsaya kan cin tarar Najeriya ne, kasancewar abinda ya faru a wasan.

Alokacin wasan bayan da Najeriya ta samu nasarar jefa kwallo ta biyu, wani ‘dan kallo kuma mai goyon bayan Super Eagles ya rantaya da gudu har cikin fili domin nuna murnar sa, wanda hakan ya sabawa dokar hukumar kwallon, har takai da cin tarar Najeriya hari dala dubu biyar kimanin Naira miliyan ‘daya da motsi.