Da farko dai sanannen mawakin nan mai suna Tupace, shine ya shirya gangamin kafin daga baya ya bada sanarwar janyewa, sai dai wasu kungiyoyi sun jagoranci zanga-zangar a biranen Legas da Abuja. Duk da yake ‘yan sanda sun hana masu zanga-zangar halartar wani maci a dandalin Unity dake Legas.
Masu zanga-zangar dai sun fito ne domin nuna rashin amicewarsu ga tsadar rayuwa da suka alakanta da manufofin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, da yanzu haka yake hutu da jinya a London.
Daruruwan masu zanga-zangar dai sun fito ne dauke da kwalaye da rubutu a jikinsu, wadanda ke nuna fushinsu ga halin da talakan Najeriya ya tsinci kansa.
Rahotanni na cewa an gudanar da ire-iren wannan zanga-zanga a wasu manyan birane na kasar da suka hada da birnin Legas da Abuja da Fatakwal na jihar Rivers.