ABUJA, NIGERIA - A hirar da wakilin Muryar Amurka Umar Farouk Musa ya yi da Alhaji Mohammed Maigari Dingyadi, wanda ya halarci taron majalisar da aka yi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya ce sun tattauna kan batun yin haramci ga kungiyoyi ko hukumomin tsaron sa-kai marasa rijista.
Daukar wannan matakin na zuwa ne bayan la’akari da cewa irin wadannan kungiyoyin da jami’an tsaron sa-kai na neman wuce gona da iri a shiga harkokin da ba nasu ba, kamar batun mallakar makamai a kasar.
Kwamiti na musamman wanda ofishin mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro na NSA, shi ke da alhakin kula da harkokin kanana da manya makamai, a saboda haka babu dalilin da zai sa wadannan kungiyoyin marasa lasi su nemi shiga harkar makamai, a cewar Dingyadi.
Duk da cewa ana bukatar gudummuwar ‘yan Najeriya wajen magance matsalolin tsaro, akwai muhimman batutuwan da ba kowa ke da hurumin shigarsu ba.
Yawaitar makamai a hannun jama’a na daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta a Najeriya ta fannin tsaro, yayin da kusan a kowanne mako sai an samu labarin kisa ko yin garkuwa da jama’a a baya-bayan nan.
Saurari hirar Umar Farouk Musa:
Your browser doesn’t support HTML5