Ministan Ruwan Najeriya, Injiniya Suleiman Husaini Adamu, ya ce a halin yanzu akwai kimanin mutane miliyan 47 da su ke bahaya a filin Allah ta’ala, al’amarin da ya sa Najeriya ta zama kasa ta biyu a duk fadin duniya wajen wannan matsalar.
Ya bayyana hakan a gurin wani taro kan albarkatun ruwa da tsabtar muhalli.
MInistan ruwan ya ce, Indiya tana da kimanin mutane miliyan 500 da su ke bahaya a fili, amma bisa kokarin da Firaiminstan Indiya ya yi cikin shekaru uku kacal an shawo kan matsalar da kashi cas’in a duk fadin kasar.
Mininstan ruwan yace mutanan Indiya sun yi bandaki sama da miliyan 80, ya kuma kara da cewa idan har Indiya za ta iya hana Mutane miliyan 500 cikin shekaru uku to ba abinda zai hana Najeriya ta hana mutanenta miliyan 47.
Sannan y ace don shawo kan wannan matsalar ya tura wasu jami’ai daga ma’aikatarsa da kuma wakilai daga jihohi zuwa Indiya don ganin yadda itama Najeriya zata dabbaka wannan tsarin yadda zai dace da ita.
A halin da ake ciki yanzu, Najeriya ta na da kananan hukumomi 774, daga cikinsu goma ne kacal inda ba a bahaya a fili.
Dr. Husaini Hassan, wanda kwararre ne kan muhalli ya ce za a iya cimma nasara idan aka maida hankali wajen fadakarwa da kuma bayyana wa jama’a illolin da ke tattare da aikata hakan.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5