Najeriya Za Ta Dauki Matakan ‘Kara Kiyaye Filayen Saukar Jiragen Saman Kasar

Filin Saukar Jiragen Sama na Murtala Muhammed International Airport Dake Lagos

Gwamnatin Najeriya za ta dau matakan rigakafi yafi magani wajen inganta lamuran tsaro a filayen jiragen kasar.

Hakan ne yasa Ministan lamurran jirage Hadi Sirika, ya yi taro da Ministan cikin gida don bayar da horo na musamman ga jami’an tsaron filayen.

Shin ko dai akwai wata barazana ne da suka hango? Hadi Sirika cewa yayi “hange ya zama wajibi, idan har mutum ba ya son ayi masa bazata, ko tashi na kamaka. San nan kuma akwai damar hukumar da take kula da harkokin jiragen saman, sai dai tana da rauni domin bata da hurumin daukar makamai domin kawo tsaro a filayane saukar jiragen kasar.”

Shi kuma Ministan cikin gida, laftanar janal Abdurrahman Danbazau Mai Ritaya, yace horon ba zai hada da tura jami’an soja ba.

A bara dai jami’ai sun damke wani da akayi zargin dan ta’adda ne a babban filin saukar jirgin sama na Abuja da aka bada labarin yan shirin kai hari ne. Tsagerun Niger Delta ma sunyi barazanar kai hare hare kan cibiyoyin gwamnati a birnin Tarayya Abuja, gabanin yanzu da gwamnati ke zantawa da su don samun masalaha, haka kuma na adawa da bin hanyar lalama.

An ruwaito ministan tsaron Najeriya Mansur Dan Ali yace ba a kawar da matakin soja ba matukar tsageran suka bijirewa tattaunawar.

Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya da ga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Za Ta Dauki Matakan ‘Kara Kiyaye Filayen Saukar Jiragen Saman Kasar - 2'48"