Kungiyoyi masu zaman kansu na musayar kalamai da ta da jijiyar wuya kan batun wasu kudade har Naira miliyan 585.198 da Ministar Ma'aikatar Agaji da Walwalar Jama'a ta ce a aika da su wani asusu na daban ba na jihohin da abin ya shafa ba.
Kungiyoyin dai sun yi kira da a hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin lamarin domin ya zama izina ga wasu.
Wasu kungiyoyi masu rajin kare hakkin ‘yan Najeriya, irinsu HURIWA a karkashin shugabanicn Emmanuel Onwubiko da NEFGAD a karkashin Akingunola Omoniyi suna ta sa toka sa katsi kan cewa ya kamata a sallami duk wadanda wannan batu na cire kudi daga asusun Ma'aikatar Kula da Agaji da Walwalar Jama'a da Ministar Ma'aikatar Beta Edu ta ba da umurnin a yi, sannan Shugaba Bola Tinubu ya hanzarta tube matan daga mukamansu.
Darakta Janar ta Kungiyar Mata Zalla daga Arewa ta Yamma, Hajiya Saratu Musawa, ta ce ba'a yi wa mata adalci, saboda ba su da yawa a mukamai shi yasa ake sa masu idanu.
Hajiya Saratu ta ce a rika yin binciken kwaf-kwaf a duk lokacin da aka samu zargi irin wannan, saboda ana iya kullawa mace sharri.
Ita ma ‘yar gwagwarmayar ganin an ba wa mata ‘yanci, Hajiya Mariya Ibrahim Baba, ta yi tsokaci cewa an haska fitila ne a wannan Ma'aikata ta Agaji da Walwalar Jama'a, inda ake da mata da dama.
Mariya ta ce dalilin da yasa ake wannan zargin ya nuna cewa akwai abin dubawa a yadda ake bibiyar laifuka irin wadannan.
Mariya ta kara da cewa dole ne ayi bincike na kwarai domin a tabbatar da gaskiyar lamarin, kuma idan an samu laifi a hukunta mai laifin, domin ya zama izina ga wasu na gaba, in ba haka ba, za yi ta zama ne kara zube.
Da yake amsa tambayar ko menene shari'a ta tanadar wa wanda ya aikata irin wannan laifin? Barista Mainasar Kogo Umar, ya ce abu ne da ke mike, domin sashi na 15 karamin sashi na 5 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya dora wajibci akan kowane jami'i na gwamnati, tun daga Shugaban Kasa zuwa Ministoci har zuwa ga Masinja cewa dole ne su yaki cin hanci da rashawa kuma su yaki amfani da kujera domin gina kai.
Mainasara ya ce sashi na 21 da 23 da 24 sun dora wajibci na rikon gaskiya da amana, saboda haka idan Shugaba Tinubu da gaske yake yi wajen yaki da cin hanci da rashawa to ya yi maza yasa rariya ya tace duk wani wanda yake da rashin tsafta a yi waje da shi, a kawo mutane nagartattu kuma ingantattun mutane masu tsoron Allah a ba su mukamai domin ci gaban kasa.
To sai dai mai magana da yawun Ofishin Akanta Janar na Kasa a Najeriya, Bawa Mokwa, ya ce akanta ba ta bi umurni biyan kudaden a wani asusu na daban ba saboda doka ba ta ba da izini a biya kudi daga Ofishin Akanta na kasa kai tsaye ba.
Mokwa ya ce an ba wa Ministar Agaji shawara cewa ta bi umurni yadda ake mu'amalar kudi a kasa.
Abin jira a gani shi ne irin matakan da Shugaban Bola Ahmed Tinubu zai dauka na ganin an warware zare da abawa a wannan batun.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5