Najeriya: Takaddama Tsakanin Fadar Shugaban ‘Kasa Da Majalisar Dattawa

A kwai alamun sake komawa ruwa tsakanin fadar shugaban kasar Najeriya da Majalisar ‘kasa, dangane da matakin da shugaba Buhari ya dauka na mayarwa da ‘yan Majalisar Dattawa sunan Ibrahim Magu, da kuma rashin sauke sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal.

Shugaban Buhari na neman Majalisa ta sake tantace Ibrahim Magu, don tabbatar da shi a matsayin shugabantar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.

Majalisar dai ta mayar da sunan Ibrahim Magu, a dalilin wani sako da ta samu daga shugaban hukumar tsaro ta SSS, na cewa yana da kalubale na zargin cin hanci da rashawa.

Shugaba Buhari dai yayi kememe da kin tunbuke sakataren gwamanatinsa Babachir David Lawal, wanda ake zargi da cin hanci da rashawa da kudaden da za a tallafawa ‘yan gudun hijirar da yaki da Boko Haram ya ‘dai ‘dai ta.

Sai dai kwararre akan ayyukan Majalisa da dokoki Farfesa Al-mustapha, yace lalle akwai hanyoyi da za a iya warware wannan matsala ba tare da kowanne bangare ya tozarta ba.

Saurari cikakken rahotan Umar Faruk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Takaddama Tsakanin Fadar Shugaban ‘Kasa Da Majalisar Dattawa - 4'27"