Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ogun: Gwamnati Zata Kare Lafiyar Masu Zuba Hannun Jari A Jihar


Gwamnatin jihar Ogun ta baiwa masu zuba jari tabbatacin kare lafiyarsu da dukiyoyinsu a jihar.

Gwamnan jihar Ibikunle Amosun, shine ya tabbatar da hakan a wajen wani taron karbar ‘dalibai da malaman makarantar sakandaren Nigeria Turkish International Colloge, guda takwas da aka sace a kwanakin baya kuma jami’an ‘yan sanda suka samosu.

Amosun yace yana maraba da duk wanda yake son zuwa yin harkoki a jihar Ogun, amma ba zuwa aikata laifi ba. yace yanzu haka sun ‘dauki matakan samar da zaman lafiya a jihar, haka kuma ya yabawa jami’an tsaron da suka gano mutanen takwas da aka sace.

A lokacin da kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Ahmed Iliyasu ke mika ‘daliban da malamansu ga gwamnan jihar, yace har yanzu suna nan suna neman sauran mutanen da sace.

‘daya daga cikin wadanda aka sace ta nuna jin dadinta tare da godiya ga wadanda suka samo su. Mutanen da aka sace sun kwashe kwanaki 11 kafin a gano inda suke.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG