Yace su a PDP suna yiwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari fatan alheri tare da yin addu'a Allah ya bashi lafiya.
A PDP suna son su karbi mulki ne ta hanyar zabe, wato a siyasance. Yace haka kuma a siyasance babu wani abun da zai shafi wani dan APC da zai tsinana masu komi a PDP. Yace tana yiwuwa 'yan adawan dake cikin APC ne suke yada jita-jitar.
Inji Ahmadu Makarfi lokacin da Umaru Musa 'Yar'Adua ya rasu ai ba jam'iyyar adawa ba ce ta karbi mulki. Saboda haka me PDP zata karu dashi idan shugaban kasa ya rasu.
Akan yin adawa Sanata Makarfi yace idan babu adawa za'a samu mulkin kama karya.Idan an cire adawa to babu mulkin dimokradiya amma injishi a yi adawa mai tsafta, ba wai a dinga sukar gwamnati ba gaira ba dalili ba. Idan gwamnati tayi abu mai kyau a yaba mata idan kuma tayi mara kyau din a soketa a kuma bada hanyar da ta fi.
Dangane da abubuwan dake faruwa a Kaduna, Sanata Makarfi ya fara ne da yiwa jama'ar Kaduna da gwamnatin jihar ta'aziya. Yace abun dake faruwa bai kamata a kawo siyasa ciki ba. A cigaba da addu'a tare da barin al'umma su samo mafita da kansu.