Najeriya, yanzu tafi kowace kasa, a Afirka, yawan ‘yan gudun hijira wadanda aka raba su da matsuguninsu, addadin da yafin miliyan uku.
Kamar yanda alkaluman cibiyar tattara bayanai akan ‘yan kudun hijira na kasa da kasa ya nuna.
Akasarin hare-haren ‘yan bindiga ne da tashe-tashen hankula ne ke raba su da gidajen lamarin da yake kara barazana ga kasar.
Wani batu dake jawo kwararan ‘yan kudun hijira ko kuma raba aluma da gidajensu shine tashe-tashen hankula dake da nasaba da fadan kabilanci ko na addini, masamman a jihohin Taraba, Benue, Nasarawa,Plateau da kuma jihar Kaduna.
Wani matsala kuma da hukumar bada agajin gaggawa ke fuskanta wajen tallafawa ‘yan kudun hijiran masamman a wuraren da ‘yan bingiga ke kai hare-hare shine na rashin tsaro da kuma rashin sanin abun da ke iya faruwa.
Your browser doesn’t support HTML5