Hukumar tace zata yi hakan ne domin su san yadda zasu yi muamala da mutane domin gujewa kamuwa da cutar.
Malam Yakubu Datti yace sun samar da likitoci a duk filin jiragen sama domin binciken masu shigowa musamman daga kasashen Afirka. Tun kafin a dauko fasinjojin sai an tabbatar cewa basu dauke da cutar. Idan kuma sun iso Legas akwai likitoci da zasu bincikesu. An kebe wani karamin dakin gwaji inda za'a kai duk wani da ya nuna alamar kamuwa da cutar. Malam Yakubu yace suna yin hakan ne domin kare lafiyar 'yan Najeriya.
Dr Nasir Isa Gwarzo shugaban yaki da hana kamuwa da cutar na kasa yace bayan lakca da ya yiwa ma'aikatan a Legas sun samar da kwamitoci har guda biyar daban daban domin yaki da cutar ta ebola. Ban da Legas har ma da sauran tashoshin da jirage ke sauka aka yiwa tanadi domin kada cutar ta shigo har ma ta yadu a kasar.
Duk wanda ya shigo kasar ta tashar Legas kafin ma ya sadu da hukumomin shige da fice ko kwastan sai kwamitin binciken cutar ya gana dashi.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa