Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yanbindiga Sun Kashe Wani Hakimi a Karamar Hukumar Ganjuwa Jihar Bauchi


Masu juyayin kisan da aka yi
Masu juyayin kisan da aka yi

Hukumomin tsaro a jihar Bauchi sun tabbatar da kisan mutane uku da wasu 'yanbindiga suka yi a garin Soro dake cikin karamar hukumar Ganjuwa jihar Bauchi

Cikin mutane uku da 'yanbindigan suka kashe har da hakimin garin Soro dake cikin karamar hukumar Ganjuwa.

Kakakin 'yansandan jihar Bauchi DSP Haruna Muhammed yace 'yanbindigan kimanin su shida suka yi kwantan bauna kafin su yiwa garin diran mikiya tare da bude wuta akan mutanen. Lamarin ya faru ne misalin karfe bakwai da minti arba'in da biyar na yammacin Asabar. Banda hakimin da suka kashe sauran mutanen biyu 'yan kasuwa ne.

Da lamarin ya faru 'yansanda sun isa garin sun kuma kewayeshi domin su kama 'yanbindigan amma hakonsu bai cimma ruwa ba kodayake wani da suka kama da can yana taimaka masu wurin gano makamai da kama wasu bata gari.

Kawo yanzu ana cigaba da bincike domin a kama 'yanbindigan.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG