Ma'aikatu da Hukumomi da dama da suka kare kasafin kudin su na shekara 2023 a gaban Majalisar Dokokin Kasar irin su Ma'aikatar Kula da tsaro da bayanan sirri, da kuma Ma'aikatar Kula da harkokin Kasashen Waje, da ma faadar shugaban kasa kanta, sun koka cewa kasafin su na shekara 2023 yayi kadan.
Shugaban Kwamitin Tsaro da Bayanan Sirri a Majalisar Dattawa Abdullahi Ibrahim Danbaba yayi karin haske cewa barin Ma'aikatu da Hukumomin tsaron kasa babu isassun kudi ba abu ne da zai haifar da, da mai ido ba, domin aiyukan tsaro na bukatan kudi,musamman ma na samo bayanan sirri.
Danbaba ya ce Majalisa za ta dauki matakin kawo wa ma'aikatun dauki ta yada doka ta tanada.
A bangaren Majalisar Wakilai kuma, takaddama ce ta kunno kai tsakanin Kwamitin kula da Ma'aikatar kasashen Waje da Ministan Ma'aikatan Kasashen wajen, inda Shugaban Kwamitin ya yi korafi cewa Ma'aikatar ba ta bin ka'idoji da aka shimfida Mata ta yadda ake kashe kasafin kudi, saboda haka Majalisa ta hana a ba su Kasafin kudin badi sai sun gyara.
Shugaban Kwamitin Yusuf Buba Yakubu ya yi baiyani cewa Majalisa ta sha aikewa ma'aikatar takardar umurnin na gyara Ofisoshin jakadancin kasa a duk fadin duniya amma sai Ministan yayi burus da wasikun. Saboda haka Majalisa ta dauki wannan mataki na dakatad da kasafin su na badi akan sai sun gyara.
Ko da yake masanan tattalin arziki na ganin akwai hanyoyi dayawa da ake bi wajen yin amfani da kasafin kudi, amma ya kamata a duba bangarorin da ake bukatan yin aiki cikin gaggawa saboda mutane su samu saukin abubuwan more rayuwa irin su ruwan sha, magunguna a asibitoci, hanyoyin sufuri, da sauran kayan masarufi.
Kwararre a fanin tattalin arziki Nasiru Marmara yana cikin masu irin wannan tunani. Marmara ya ce masana'antu za su zo su kafa ma'aikatu ne idan akwai ababen more rayuwa idan an yi amfani da kasafin kudi yadda ya kamata.
Hakazalika, Marmara ya ce yin amfani da Kasafin kudi yana zama wata matakala ne na kawo wa kasa kudi sannan kuma a kashe su ta hanyar da ta dace.
Ma'aikatu da Hukumomin Gwamnati na cigaba da kare Kasafin kudin su na shekara 2023 a gaban Majalisar Dokokin kasar ne har zuwa ranar 15 ga wannan wata da muke ciki.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5