Hukumar tace ta kama mutanen ne a dalilin rashin takardun zama a Najeriya, kuma tuni ta iza keyarsu zuwa kasar Nijar, shugaban hukumar mai kula da jihar Neja, Mr. David Adi, yace tun da farko sun cafke mutane 500, amma bincike ya nuna sauran mutanen na da takardun izinin zama a kasar.
Shugaban kungiyar yan Nijar mazauna jihar Neja, Alhaji Magaji Shu’aibu, ya nuna takaici akan wannan kame da akayiwa yan kasar tashi, inda yace ya ziyarcesu kuma wasunsu da dama suna da takardunsu amma aka aza keyarsu zuwa Nijar.
Sakataren kungiyar yan Nijar dake zaune a jihar Neja, Alhaji Umar Ahmad, yace suna fadakar da mutanensu mahimmancin yin takardun domin kaucewa shiga matsala. Anyi amfani da motocin dakon kaya wajen daukar ‘yan Nijar din zuwa kasar jamhuriyar Nijar.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5