Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Ta Kaya Game Da Kai Hama Amadou Jinya Zuwa Turai


An dauki dan takarar jam’iyar hamayyar Jamhuriyar Nijar Hama Amadou daga gidan yari da ake tsare dashi a Niamey zuwa wani asibiti a birnin Paris jiya Laraba, ana sauran kwana hudu a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.

An tsare Hama Amadou a gidan yari tun watan Nuwamba bisa zargin safarar jarirai, zargin da shi da magoya bayansa suce ce bita da kullin siyasa ne.
Jami’an hamayya sunce Amadou ya jima yana fama da rashin lafiya tunda aka daure shi, sai dai ba a san ainihin abinda ke damunsa ba.

Hama Ahmadou tsohon kakakin majalisa , yana so a sa sunansa a katunan zaben da za a gudanar ranar Lahadi ko da yake makon jiya, gamayyar kungiyoyin hamayya da yake jagoranta suka yi barazanar kauracewa zaben

Suna zargin cewa, sakamakon zaben da shugaban kasa mai ci yanzu Mahamadou Issoufou ya lashe na boge ne.

Gamayyar jam’iyun hamayyar sun kuma zargin kotun kolin kasar da hada baki da gwamnati da nufin ganin an sake zaben shugaba Mahamadou Issoufou. Suna zargin shugaban kasar da mulkin kama karya.

Duk da albarkatun makamashi da Nijar ke da shi, tana daya daga cikin kasashen da suka fi talauci a duniya.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG