A yau ne aka fara taron na kwanaki biyu, wanda shugaba Muhammadu Buhari ke jagorantar. A jawabinsa, shugaba Muhammadu Buhari ya tunar da jama’a akan cewa “zaben da aka yi a kasar Burkina Faso ya cika kammaluwar zabuka na shekarar 2015 a wannan shiyar, an yi zabe cikin lumana a kasashen Najeriya, Togo Guinea da kwadebuwa”.
Wannan gagarumar nasarar na nuna irin kudurinmu na bai daya wajen inganta demokradiyya da kyakyawan inganci a wannan shiyar a cewar shugaba Buhari .
Shugaba Muhammadu buhari ya cigaba da cewa, yanzu da muke tunkarar wasu zabukan a wasu kasashen a yammacin Afrika, ina tabbatar ma ku da cewa Najeriya za ta cigaba da zakewa ga tsari irin na demokradiyya da kyakyawan shugabanci don ta haka ne shiyar Afrika ta yamma za ta sami kwanciyar hankali irin na siyasa.
Shugaban kasar Senegal, wanda kuma ke jagorancin kungiyar ta ECOWAS Macky Sall ya yabawa kasashen akan yadda suka fatattaki cutar Ebola da kuma yadda suke yaki da ta’addanci a dukan sassa.
Sai dai galibin shugabannin kasashen basu sami halartar wannan taron ba don yawancin su suna can birnin Paris don halartar wani babban taro akan sauyin yanayi.
Ga rahoton daga Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5