Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kafa Wani Kwamiti a Majalisar Wakilai Don Gano Musabbabin Tashin Hankalin Garin Zariya


Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin adadin rayukan da suka salwanta a lokacin rikin garin Zariya tsakanin sojojin Najeriya da mabiya Mazahabar Shi'a.

Ta bangarori daban-daban ana kafa kwamitoci don binciken makasudin arangamar da ta faru tsakanin sojoji da ‘yan shi’a, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a garin Zariya, jami’ai sun bada tabbacin cewa shugaban na ‘yan Shi’a Sheikh Ibrahim Al-Zakzaki ya na nan lafiya. To shin ko wane mataki za a dauka nan gaba, ma’ana zasu sake shi ne ko za su cigaba da garkuwa da shi har sai sun gama kammala kan hujjuoji don gurfanar da shi gaban kotu.

Shugaban kwamitin labarai na majalisar wakilai Abdulrazak Namdas, ya ce kwamitin majalisar zai shiga bincike don gano dukan bayanai, Kuma za su bayyana wa duniya abinda majalisar tarayyar ta gano tare da daukar mataki don tabbatar da cewa ba a sake samun irin haka ba.

A nasa bangaren, masanin harkokin tsaro Kabiru Adamu, ya ce da alamu an yi amfani da karfin da ya wuce kima, kai tsaya dai bai dora wa sojoji alhakin bude wuta bayan samun tunzura ba. Ya kara da cewa an yi kuskure a bangaren wadanda suka tare hanyar da kuma matakan da sojojin suka dauka.

Kabiru Adamu ya ce a sha’anin doka akwai tsarin da ya kamata su bi akan abin da ya danganci farar hula don ba sa dauke da makami.

Cikin wadanda aka tabbatar da rasuwarsu akwai Buhari Bello Jega na jami’ar Abuja wanda kan yi wa sashen Hausa sharhi akan lamuran siyasa musamman ma a lokacin zabe.

Ya zuwa yanzu dai babu takamaiman bayani ko adadin wadanda suka rasa rayukansu a lokacin wannan tashin-tashinar.

Ga karin bayani daga Nasiru Adamu El-hikaya

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Labarai masu alaka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG