Najeriya ta Kulla Yarjejeniya da Faransa

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sa hannu a wata sabuwar yarjejeniya da kasar Faransa a fannonin aikin soja, da ayyukan noma da kuma wutar lantarki.

Shugaban Najeriya da takwaransa na kasar Faransa Francois Holland sun sa hannu a yarjejeniyar ne yau, kafin bude taron koli kan harkokin tsaro dake kankama a birnin tarayya Abuja.

Kasar Faransa ta amince zata taimakawa Najeriya ta fannin horas da jami’an tsaro da samar da bayanan leken asiri ,da kuma wadansu dabaru yaki, a yunkurin kakkabe mayakan kungiyar Boko Haram.

Har wa yau, kasar Faransa zata tallafa a fannin ayyukan noma da nufin rage dogaro ga albarkatun man fetir da Najeriya ke yi, ganin yadda ake ci gaba da samun faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Faransa zata kuma taimaka a fannin ayyukan wutar lantarki da ake kyautata zaton zai taimaka gaya wajen farfado da masana’atun kasar da suka durkushe da kuma samar da ayyukan yi musamman tsakanin matasa.

Ga rahoton da wakilinmu Umar Faruk Musa ya aiki daga Abuja, Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya ta kulla yarjejeniya da Faransa-2:12"