‘Yan sandan sun dirarwa da’irar ‘yan ta’addan ne a arewacin birnin Tunis, wajen da ‘yan ta’adda daga wasu kasashe suka hadu don shirya abinda jami’an tsaron suka kira da ‘Shiryayyun Hare-hare’.
An kashe ‘yan ta’adda biyu aka kuma cafke guda goma sha shida. Jami’an sun ki bada dogon bayani game da kai samamen ko kuma harin da ake kitsawa din, to amma sun tabbatar da kwace makaman da suka hada da bama-bamai da wasu nau’in daban.
Jami’an tsaron har ila yau sun kai wani samamen daban a Tataouine dake Kudancin Tunisiya duk a jiya Larabar. Inda ‘yan sanda hudu suka rasa ransu a lokacin da wani daga cikin ‘yan ta’addan yayi damara da bel din bam ya tarwatsa kansa.
Tunisia ce kasar Afirka ta Arewa da ta hambarar da gwamnatin kama karya a boren Larabawa na shekarar 2011. To sai dai har yanzu, tsattauran ra’ayi da ta’addanci yana wahalar da siyasar kasar. Ko a bara sai da 'yan ISIS suka kai hari wata mashakatar bakin teku da wani gidan tarihi, har mutane 60 da yawanci ‘yan yawon bude ido ne daga kasashen waje suka mutu.
Haka kuma a watan Maris sai da ‘yan ta’addan kasar hade da na ketare daga Libya suka fafata fada da jami’an tsaro a Kudu maso Gabashin kasar, inda fararen hula bakwai da jami’an tsaro da ma wasu ‘yan ta’addan suka mutu.