Najeriya Ta Karya Darajar Naira

Naira, kudin Najeriya

Gabanin wannan sauyi na baya-bayan nan, Najeriya ta sha bin tsaruka daban-daban wajen kayyade farashin dala, a wani mataki na kaucewa karya darajar naira.

Babban bankin Najeriya ya karya darajar naira ta hanyar cire kayyadaden farashin dala daga 379 da aka saba canzawa a harkokin kasuwanci.

Rahotanni sun ce daga yanzu za a rika canza dalar ne akan naira 410.25 kamar yadda babban bankin ya wallafa a shafinsa.

Hakan na nufin farashin dalar zai kasance bisa tsarin yadda kasuwa ta yi halinta.

A makon da ya gabata VOA ta ruwaito kwararru a fannin tattalin arziki na gargadi kan yadda tsame hannun bankin na Najeriya a harkar canja dala zai yi tasiri kan farashin kayayyaki.

“Illar wannan ga halin da muke ciki a Najeriya shi ne, na farko, muna fama da hauhawan farashin domin abubuwan da muke amfani da su shigo da su mu ke yi. Saboda haka, hauhawna farashin zai karu.” In ji Malam Abubakar Ali, masanin tattalin arziki.

Mafita a cewar Ali ita ce, dole na a dawo daga rakiyar dogarao da kayayyakin kasashen waje.

Shi ma masanin tattalin Arziki, Yusha’u Aliyu ya bayyana tasa fahimta da matakin na babban bankin Najeriya ya dauka.

“Lokacin da masu bukatar dala suka yawaita, farashin dala zai hau, haka kuma duk lokacin da bukatun kudaden waje ya ragu farashin zai ragu.” In ji Yusha’u Aliyu.

Gabanin wannan sauyi na baya-bayan nan, Najeriya ta sha bin tsaruka daban-daban wajen kayyade farashin dala, a wani mataki na kaucewa karya darajar naira.