Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsame Hannun CBN A Harkar Canji Zai Kara Hauhawar Farashin Kayayyaki A Najeriya - Masana


Kudaden dalar Amurka
Kudaden dalar Amurka

Hakan na nufin cewa, farashin da ake sayar da dala a kasuwanni bayan fagge za’a ci gaba da amfani da shi na naira 480 kowacce dala 1 daga yanzu.

Masana tattalin arziki a Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa game da batun daidaita farashin dala da babban bankin kasar wato CBN ya yi bayan cire farashin kowacce dala dake ke kan naira 381 a hukumance daga bankunan kasar.

Hakan na nufin cewa, farashin da ake sayar da dala a kasuwanni bayan fagge za’a ci gaba da amfani da shi na naira 480 kowacce dala 1 daga yanzu.

Babban bankin Najeriya dai ya bayyana cewa, ya tsame hannun daga batun kayyade farashin dala a hukumance daga bankunan cinikayyar kasar domin daidaita al’amura a fannin canjin kudi a kasar.

Sai dai tun bayan sanar da hakan ne masana tattalin arziki a kasar ke ta bayyana damuwa game da lamarin.

“Illar wannan ga halin da muke ciki a Najeriya shi ne, na farko, muna fama da hauhawan farashin domin abubuwan da muke amfani da su shigo da su mu ke yi. Saboda haka, hauhawna farashin zai karu.” In ji Malam Abubakar Ali, masanin tattalin arziki.

Mafita a cewar Ali ita ce, dole na a dawo daga rakiyar dogarao da kayayyakin kasashen waje.

Shi ma masanin tattalin Arziki, Yusha’u Aliyu ya bayyana tasa fahimta da matakin na babban bankin Najeriya ya dauka.

“Lokacin da masu bukatar dala suka yawaita, farashin dala zai hau, haka kuma duk lokacin da bukatun kudaden waje ya ragu farashin zai ragu.” In ji Yusha’u Aliyu.

Kafin matakin na babban bankin Najeriya dai, farashin kowacce dala a bankunan cinikayya na kan naira 381.

Da muka tuntubi babban bankin kasar, daya daga cikin masu magana da yawun bankin wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar da batun tsame hannun daga hada-hadar kudin waje.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG