Najeriya Ta Kara Kaimi A Yaki Da 'Yan Ta'adda - Inji Shugaba Buhari a MDD

SHUGABA MUHAMMADU BUHARI

A ranar Talatar makon jiya ne shugabannin kasashe da shugabannin gwamnatoci suka fara jawabai a mahawarar babban taron kolin Majalisar Dinkin Duniya na cikon shekaru 76 a birnin New York.

Batutuwa kamar sauyin yanayi, COVID-19, da kuma tsaro ne suka dauke hankali a jawaban shugabannin da wasunsu suka halarci taron bayan sama da shekara guda da annobar coronavirus ta tilasta wa duniya gudanar taruka ta yanar gizo.

A wannan ranar Talata, shugabannin duniya, kamar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, da shugaban Amurka Joe Bide da Shugaban China Xi Jinping da kuma shugaban Iran Ebrahim Raisi suka fara yin jawaban su.

Batun tsaro shine babban abu da galibin shugabannin Afrika suka yi ta yin Magana akai, yayin da ya yi na sa jawabi, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa a kan safara da aikewa da kuma yada kananan makamai, ya ce duk inda aka samu yawan wadannan makamai a duniya suna mummunan tasiri a kan tattalin arziki da zamantakewa musamman a Afrika.

A kan batun ta’addanci kuwa shugaba Buhari cewa ya yi ta’addanci na ci gaba da zama matsalar tsaro a duniya, a Najeriya koda yake sojojin mu sun runan kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram, kungiyar na nan na gudanar da ayyukanta.

Shugaba Buhari ya kara da cewa Najeriya zata ci gaba da aiki da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya masu yaki da ayyukan ta’addanci. Yace Najeriya ta kar kaimi wurin yaki da wannan mummunan aiki kana zata yi amfani da kowa ce hanya domin yaki da ‘yan Boko Haram a arewa maso gabas da yankin tabkin Chadi da kuma ‘yan bindiga a arewa maso yamma da da maso tsakiyar Najeriya.

Gwamnan Zamfara Bello Mutawalle da shi kuma ya halarci taron na Majalisar Dinkin ya bayyana irin tasirin da matakan yaki da ‘yan bindiga da gwamnatinsa ta dauka su ka yi.

Ga rahoton Baba Yakubu Makeri daga birnin New York:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ta Kara Kaimi a Yaki da Ta'addanci