Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Majalisar Dinkin Duniya: Yadda 'Yan Najeriya Suka Yi Zanga Zanga A Birnin New York


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)

Wasu 'Yan Najeriya sun gudanar da zanga zangar nuna goyon bayan kasar ta ci gaba da zama kasa daya dunkulalliya da masu neman a yi zaben raba gardama a gaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke brinin New York na Amurka.

Dubban mutane da suka saba halartar wannan taro da ke tattaro shugabannin kasashen duniya ba su samu damar yin haka sai ‘yan kalilan saboda matakan da duniyar ke dauka a kan annobar coronavirus.

An gudanar da taruka da dama ciki har da batun sauyin yanayi, da annobar COVID-19 musamman batun rashin daidaito wurin raba allurar rigakafi da taro a kan makaman nukiliya da batun Shirin Muradun karni da kuma tallafa wa kasashe masu tasowa.

Wata al’ada da aka saba gani a wannan taro ita ce gudanar da zanga zanga a kan damuwa da mutane ke da ita a kasashensu da zummar duniya za ta shaidi halin da ake ciki a kasashen nasu.

Wasu ‘yan Najeriya sun gudanar da zanga zanga a gaban ofishin jakadancin Najeriya da ke kusa da ginin Majalisar Dinkin Duniya inda ake gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76.

Shugaban masu zanga zangar son Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya, Mallam Hassan Sallau Jibiya, ya ce wannan zanga zangar sun yi ta ne domin su fito su nuna goyon baya ga kasarsu Najeriya da kuma kira gara a zauna kasa daya al’umma daya da ace za a raba kasa kashi kashi.

Jibiya ya kara da cewa saboda yanzu idan ka ce zaka raba Najeriya baka ma san ta inda za ka fara ba to shine yasa idan ba a fito aka nuna cewa akwai mutanen da su ke so ainihin Najeriya ta zauna kasa daya al’umma daya kuma cewa akwai abin kirki da ake yi ba to ba za a samu cimma manufa ba, to shi yasa suka hada wannan taro saboda duniya ce ta taru a birnin New York.

Ya ce arewacin Najeriya ya fi fuskantar matsalolin tsaro fiye da yankin kudancin kasar kuma maganar fulani da ke sace mutane da kashe su ta fi kamari a arewacin kasar.

Rev. Mrs. Folunso Arileba ta kungiyar Yoruba Nation ta ce zaman Najeriya dunkulalliyar kasa wata yaudara ce, kasuwanci ne ake yi da kasar saboda yarjejeniyar shekaru 100 da ta hada bangarorin Najeriya wuri guda a shekarar 1914 ta kare a shekarar 2014 shekara 100 sun cika cif.

Rev. Arileba ta kara da cewa manufar zanga zanga da kungiyar ta Yoruba Nation ke yi shi ne suna bukatar zaben raba-gardama ne yanzu saboda waccan yarjejeniyar ta kare tun shekarar 2014.

Ta ce ka je Najeriya ka ji abin da mutane ke fadi, ana kisan kakkabe kabila ana kisan kare dangi, Buhari ya kawo Fulani daga wurare daban daban na Afurka ta Yamma suna kwace mana garuruwanmu, babu wanda ya isa ya tsoratar da mu.

Bangarorin biyu da ke zanga zangar ki da son yadda Najeriya ke zaune suna nan suna ci gaba da gudanarwa har sai baba tagani.

Saurari cikakken rahoton Baba Yakubu Makeri:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG