Gwamnatin Najeriya ta bukaci ‘yan kasar da su kula matuka tare da gujewa tafiya kasar Birtaniya saboda abin da ta ce akwai yiwuwar karuwar rikici biyo bayan tarzoma da ta barke a kasar saboda kisan wasu ‘yan mata uku a wani taro.
Wannan na dauke ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya Amb. Eche Abu-Obe ya sanyawa hannu, inda ya ce “ rikicin ya dauki wani salo mai matukar hadari, yadda aka ga yadda masu rikicin ke kai hari ma jami’an tsaro tare da fadawa kayayyaki gwamnati.”
Haka zalika ya shawarci ‘yan Najeriya a Birtaniyar da su guji zuwa taron siyasa, zanga-zanga ko wani gangami da ke da mutane da yawa.
Wasu ‘yan kasar ta Birtaniya masu tsananin ra’ayin mazan jiya suke zanga-zanga wacce ta haddasa kara kyama ga baki.