Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasa 28 da za ta tura gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a kasar Kamaru.
Za a fara gasar daga ranar 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga watna Fabrairun shekarar 2022.
Kocin Super Eagles Agustine Eguavoen ne ya zabi sunayen ‘yan wasan, wanda Ahmed Musa zai jagoranta a matsayin kyaftin.
Najeriya, wacce ta taba lashe kofin gasar sau uku, na rukuni daya da Masar da ta taba lashe kofin gasar sau bakwai, sai Sudan da kuma Guinea Bissau da za ta je gasar a karon farko.
Najeriyar za ta fara karawa ne da Masar a wasansu na farko a arnar 11 ga watan Janairu.
Ga jerin ‘yan wasan da Najeriya ta fitar:
Masu Tsaron Raga
Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs FC, Afirka ta Kudu)
Frabcis Uzoho (AC Omonia, Cyprus)
John Noble (Enyimba FC, Najeriya)
Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, Netherland)
Maso Tsaron Gida
William Ekong (Watford FC, Ingila)
Kenneth Omeruo (CD Leganes, Sifaniya)
Leon Balogun (Ranger FC, Scotland)
Abdullahi Shehu (AC Omonia, Cyprus)
Chidozie Awaziem (Alanyaspor FC, Turkiyya)
Jamilu Collins (SC Paderborn 07, Jamus)
Ola Aina (Torino FC, Italiya)
Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal)
Olisa Ndah (Orlando Pirates, Afirka ta Kudu)
‘Yan Wasan Tsakiya
Wilfred Ndidi (Leicester City FC, Ingila)
Kelechi Nwakali (SD Huesca FC, Sifaniya)
Chidera Ejuke (CSKA Moscow, Rasha)
Frank Onyeka (Brentford FC, Ingila)
Joe Aribo (Rangers FC, Scotland)
‘Yan Wasan Gaba
Ahmed Musa (Fatih Karagumruk, Turkiyya)
Moses Simon (Nantes FC, Faransa)
Odion Ighalo (Al Shabab Riyadh, Saudiyya)
Taiwo Awoniyi (Union Berlin FC, Jamus)
Alex Iwobi (Everton FC, Ingila)
Sadiq Umar (Almeria FC, Sifaniya)
Kelechi Iheancho (Leicester City FC, Ingila)
Samuel Chukwueze (Villarreal CF, Sifaniya)
Emmanuel Dennis (Watford FC, Ingila)