Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta raba gari da mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar kasar ta Super Eagles Gernot Rorh.
NFF ta nada Mr. Augustine Eguavoen a matsayin kocin wucin gadi a cewar wata sanarwa da shafin Super Eagles na Facebook ya wallafa.
“Wannan sauyi zai fara aiki ne nan take, bayan da aka kawo karshen hulda da Gernot Rohr.” In ji sanarwar.
Sama da shekara biyar Rohr ya kwashe yana horar da ‘yan wasan na Super Eagles, shi ne kuma kocin da ya fi kowane dadewa a wannan mukami.
“Hulda tsakanin hukumar NFF ta Najeriya da Mr Rohr ta zo karshe. Muna mika godiyarmu a gare shi bisa ayyukan da ya yi wa Super Eagles da Najeriya.” Babban Sakatare janar na NFF Dr. Mohammed Sanusi ya ce cikin sanarwar.
Kazalika hukumar ta NFF ta ce Eguavoen zai yi aiki da Salisu Yusuf, Paul Aigbogun, Joseph Yobo Dr Terry Eguaje da Aloysius Agu.
Sannan an nada tsoffin kyaftin din Super Eagles da suka hada da Jay Jay Okocha, Nwankwo Kanu, Garba Lawal a matsayin wadanda za su rika ba tawagar shawara.
Eguavoen, wanda tsohon kyaftin din kungiyar ta Super Eagles ne, ya kasance kocin kungiyar a lokacin da Najeriya ta zo ta uku a gasar cin kofin nahiyar Afirka a 2006 da aka yi a Masar.
Yana kuma cikin tawagar ‘yan wasan da suka lashe kofin gasar cin kofin nahiyar a karon farko shekaru 27 da suka gabata.