Najeriya Ta Fara Gasar Kwallon Kafar Mata ‘Yan Kasa Da Shekaru 17 Da Kafar Dama

Women's U17 World Cup

 A jiya Laraba Najeriya ta fara gasar cin kofin duniyar mata ‘yan kasa da shekaru 17 inda ta lallasa tawagar kasar New Zealand da ci 4 da 1.

Flamingos ta fara zagayen farko na fafatawar da karsashi, inda jefa kwallaye 3 a raga da suka bata damar tsallakawa zagaye na gaba na gasar a jamhuriyar Dominican.

Shakira Moshood ce ta jefa kwallon farko a minti na 2 da take wasan na rukunin A. kwawawan hare-haren da Flamingos din Najeriya din ta yi ta kaiwa ya bata damar cin kwallaye 3 cikin mintuna 30 da take wasan ta hannun Taiwo Adegoke da Faridat Abdulwahab.

Ana dawowa zagaye na 2 na wasan ne, Flamingos ta kara kwallo guda ta hannun Taiwo Afolabi abin da ya sauka sakamakon fafatawar zuwa ci 4-0.