Najeriya Ta Cika Shekaru 60 Da Samun 'Yancin Kai

Nigerian flag

Duk da matsin tattalin arziki da yawan sanyin guiwa da ‘yan Najeriya ke nunawa, hakan bai hana gwamnatin da jama’a daukar cika shekaru 60 da samun ‘yanci abu mai muhimmanci ba.

Tun daga samun ‘yancin an samu juyin mulki da a ka zubar da jini musamman na 1966 da sojoji bisa ma’aunin kabilanci su ka yi kisan gilla ga wasu daga manyan wadanda su ka karbo ‘yanci kamar firaminista Abubakar Tafawa Balewa, firimiya Sir,Ahmadu Bello da Ladoke Akintola inda shugaban farko Nnamdi Azikwe ya tsallake rijiya da baya.

Nigeria Aguiyi Ironsi

Juyin mulkin farko ya haddasa yakin basasa bayan ‘yan watanni da mulkin soja na Janar Aguiyi Ironsi inda Janar Yakubu Gowon ya hau gado da zummar hada kan kasa kuma har yanzu ya ke cigaba da kamfen din hana bangara kasar don kafa Biafra.

bukukuwan-cikar-najeriya-shekara-59-da-samun-yanci

kasar-najeriya-ta-cika-shekaru-58-da-samun-yancin-kai-daga-kasar-ingla

tsaro-halin-da-najeriya-ke-ciki-a-shekara-59-

Shugabannin addini, na al’umma da dattawa na nuna bukatar koyi da iyayen kasa da yawanci suka kwanta dama.

Wasu Mata a Lagos cikn shiga irin ta al'adar su suke murnan cika shekaru 55 da samun yancin Najeriya

Cikin shekarun 60 kusan an yi canjaras`na shekarun mulki tsakanin sojoji da farar hula, sojoji sun shafe kimanin shekaru 30 kan mulki inda farar hula su ka yi mulki na tsawon shekaru 30 duk da yake biyu daga sojojin da su ka yi mulki sun rikide farar hula su ka sake hawa mulki.

Sabuwar dimokradiyya daga 1999 zuwa bana 2020 ita tafi tsawo a tarihin Najeriya bayan ta farko da ta shekara 6 kacal, yayin da a ka samu shekaru 4 a jamhuriya ta biyu, kafin kifar da gwamnatin marigayi shehu Shagari bayan lashe wa’adi na biyu a 1983.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya cikin sauti

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ta Cika Shekaru 60 Da Samun 'Yancin Kai-4:00"