A rana mai kamar ta yau ne dai Najeriya ta samu ‘yan cin kai daga turawan mulkin mallaka wato a ranar daya ga watan Oktoban shekarar 1960.
Kuma duk da wasu matsalolin da aka fuskanta a baya kamar yakin basasa, Najeriya dama ‘yan kasar na zaune ne cikin kwanciyar hankali ba tare da fargaba ba na matsalar tsaro, lamarin da yanzu ke hana jama'a barci.
Wasu ‘yan Najeriya mazauna arewa maso gabas sun ce ana fama da matsalar tsaro duk da dai matsalar tsaron kashi biyu ce, matsalar Boko Haram wadda yanzu an samu saukin hare-haren da suke kai wa a wasu jihohi, amma matsalar satar mutane kuma tana addabar mutane a yanzu.
Amma wasu suna ganin an samu sauki a wasu bangarori sosai.
A baya dai ba'a da yawan jami'an tsaro da ake da su a yanzu, kuma hakanan ma kudade da kuma kayayyakin aikin da akan bai wa jami'an tsaron ba su kai na yanzu ba, to amma kwalliya ta kan biya kudin sabulu.
Wani tsohon jami'in dan sanda mai suna ASP Yakubu ya ce idan ana maganar ci gaba a cikin shekaru 59 da samun ‘yanci idan ka duba shugabanin da suka gabata suna kishin kasa ne ba wai suna kishin aljihunsu ba ne.
ASP Yakubu ya kara da cewa, yanzu ana kashe kudade da yawa amma wasu suna saka son zuciya, inda a zamanin da suka yi aiki jami’an tsaro suna kokarin su cimma burinsu na tabbatar da tsaro, kamar yadda gwamnati take kokari ta ga ta inganta harkar tsaron.
Ba kamar shekarun baya ba, a bana bikin samun ‘yancin kan ya zo ne a wani yanayi na ba sabon ba, batun da manazarta ke ganin akwai abun dubawa.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola:
Facebook Forum