Yayin da a yau yan Najeriya ke bukukuwan cika shekaru 60 da samun yancin kai ra’ayoyi sun bambanta game da nasarori da kuma akasin hakan da aka samu a wadannan shekarun.
A wannan rana ta Alhamis ce ma dai Najeriya ke cika shekaru 60 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka, wato ta samu yancin ne a ranar daya ga watan Oktoban shekarar 1960. Kuma tun bayan samun yancin kan Najeriya ta samu Shugabanni da dama, kama daga na soji da kuma na farar hula, wadanda kowannensu ya zo da salonsa.
Kama daga Firaministan farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa wanda ya ce, "Mu 'yan Najeriya mu na alfahari da fifikon da mu ke da shi sakamakon girmar kasarmu da kuma yawan mutanenta; to amma ba mu da wata niyya ta takala ko muskalazaratun," zuwa Shugaba Olusegun Obasanjo mai cewa, "Ba za mu yi kasa a gwiwa ba," zuwa Shugaba Umar Musa 'Yar'aduwa mai cewa, "Buri na shi ne in tabbatar da cikakkiyar kwanciyar hankali da tsaro," zuwan Shugaba Goodluck Jonathan mai cewa, "Babu wani burin mulki da ya kai jinin dan Najeriya daraja," zuwa Shugaba Buhari mai cewa, "Ni na kowa ne, kuma ni ba na wani kadai ba ne," duk sun daka rawarsu a idon talakan Najeriya.
Yayin da ake cigaba da bukukuwan zagayowa ta 60 ta ranar da Najeriya ta samu 'yancin kai, 'yan Najeriya - musamman ma talakawan kasar - sun bayyana mabanbantan ra'ayoyinsu kan yadda ake tafi da Najeriyar. Wasu sun yaba, wasu sun kushe, wasu kuma sun ce abin dai ba yabo ba fallasa.
Ga Ibrahim Abdul'aziz da cikakken rahoton:
Facebook Forum