Da ya ke tarbar sakatariyar, ministan tsaron Najeriya Manjo Janar Bashir Magashi, ya bayyana cewa za a kara ingancin hukumar tsaron sararin samaniyar kasar da fasahar zamani ta hanyar yarjejeniyar aiki da hukumar tsaron sararin saman Amurka don shawo kan matsalar tsaro da ta dabaibaye Najeriya a halin yanzu.
Janar Magashi ya ce ingancin kyautata tsaron sararin samaniya wani ginshiki ne na aikace-aikacen sojojin Najeriya da sauran jami'an tsaron kasar a kokarin da ake yi na kawo karshen ‘yan ta'adda da ‘yan bindiga dadi a sassan kasar, saboda haka ya yi kira ga Amurka da ta hanzarta kammala kera mata manyan jiragen yakin zamani wato A29-Super Tucano da Najeriya ta yi odarsu.
Ministan ya ce manyan jiragen yakin zasu taka rawa wajen kara ganowa, tare da afkawa maboyar ‘yan ta'addan a cikin dazuzzuka. Ya na mai jaddada cewa gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da karfafa dangantakar tsaro da Amurka musamman a fannonin musayar bayanan sirri, horaswa, musayar jami'ai da kuma sayen kayan yaki.
Tun farko a jawabin da ta yi, Ms. Barrett, wacce ita ce mace ta hudu da ta rike wannan matsayin kuma ita ke da alhakin lura da al'amuran dakarun saman Amurka da ma tsaron sararin samaniyar kasar, wacce kuma ta sami rakiyar jakadiyar Amurka a Najeriya, ta bayyana irin sha'awar da Amurka ke da shi akan Najeriya wajen alakar aikin tsaron sararin samaniya ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Berrett ta jaddada cewa irin wannan alakar ta aiki tare tsakanin kasashen biyu babu tantama za ta taimaka sosai wajen ganin Najeriya ta amfana ta fannin tsaro.