A yayin da Najeriya da sauran kasashen duniya ke ta kokarin fitar da 'yan kasar daga Sudan inda rikici yaki ci-yaki cinyewa.
Gwamnatin Najeriya tace hukumomin kasar Masar sun ki baiwa 'yan kasashe daban-daban da suka kai akalla dubu bakwai (7000) wadanda suka hada da ‘yan Najeriya, damar shiga kasar bayan isarsu iyakar Sudan da Masar jiya Alhamis.
Shugabar Hukumar kula da 'yan Najeriya dake kasashen waje ta Najeriya NIDCOM Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana haka a wata rubutacciyar sanarwa i da ta fitar yau Juma’a.
A cikin sanarwar, Madam Abike ta bayyana cewa, “Najeriya na kira ga dukkan wadanda abin ya shafa kan shige da fice a iyakokin Sudan, da su baiwa ‘yan kasashe da dama harda ‘yan Najeriya da suka kai dubu bakwai damar shiga don isa inda suke son isa.”
Ta kara da cewa, Ofishin Jakadancin Najeriya dake Masar na iya kokarinsa don ganin ‘yan Najeriya sun shiga kasar ta Masar, yadda za a iya dauko su zuwa Najeriya, amma hukumomin kasar Masar sun yi kememe suna cewa, dole sai kowanne dan Afrika da zai shiga kasar ya mallaki izinin shiga kasar wato visa sannan zai sami damar shiga don wucewa zuwa kasarsa.
Shugabar Hukumar kula da 'yan Najeriya dake kasashen waje ta Najeriya ta kuma yi kira ga hukumomin kasar Masar a sanarwar inda ta ce, “Muna rokon hukumomi Masar dasu baiwa wadannan matafiya dake cikin dimuwa damar shiga don su sami damar wucewa kasashen su dake nahiyar Afrika.”
Ku Duba Wannan Ma Gwamnatin Najeriya Za Ta Fara Kwaso 'Yan Kasar Da Ke Makale A Sudan~Alhassan Bala~