Cikin wata sanarwa da kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya rabawa manema labarai a ranar Talata, Shugaban na Najeriya ya ce, akwai bukatar Amurka ta sauyawa hedikwatar rundunar sojin wanzar da zaman lafiya a Afirka ta AFRICOM matsuguni.
A cewar Buhari, yin hakan, zai taimaka wajen kaucewa yaduwar matsalolin tsaro a yankin.
Yanzu haka hedikwatar AFRICOM na birnin Stuttgart na kasar Jamus.
Shugaban na Najeriya ya mika wannan kokon bara ne ga Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a ranar Talata, yayin wani taro da suka ta yanar gizo.
Taron ya mayar da hankali ne kan karfafa dagantakar Amurka da Najeriya da kuma yadda kasashen biyu za su fuskancin muradunsu.
“Kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya, babban abin damuwa ne, saboda abubuwan da ke faruwa a yankunan Sahel, tsakiya da yammacin Afirka da kuma yankin Tafkin Chadi.” Sanarwar Garba Shehu ta ce.
Buhari ya kara da cewa, Najeriya da jami’an tsaronta, sun himmatu wajen ganin sun shawo kan musabbabin wadannan matsaloli duk da irin girmansu.
Amma, “goyon bayan muhimman kawaye irinsu Amurka, abu ne da ba za a gaji da nanatawa ba, saboda sakamakon da rashin tsaro zai haifar, zai iya shafar dukkan kasashe.”
“Hakan ya sa, ya zama abu mai muhimmanci, kasashe su hada karfi da karfe don a shawo kan wannan kalubale.”
Hakazalika yayin taron, Buhari ya yabawa kiran taron koli kan sauyin yanayi da Shugaban
Amurka Joe Biden ya yi a makon da ya gabata, yana mai cewa, hakan wata manuniya ce da ke bayyana amincewar Amurka ga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris.