Bincike ya tabbatar da cewa ana hada-hadar kasuwancin dabino na dalar Amurka biliyan 1 da miliyan 600 a duniya, kasar Masar ce ke kan gaba wajen samar da dabino a duniya.
Najeriya ita ce kasa ta 10 wajen amfani da dabino a duniya amma kuma ta na samar da kashi 20 ne kacal cikin 100 na yawan dabinon da ta ke bukata yayin da ake shigowa da kashi 80 daga kasashen waje.
Dr. Hussaini Dikko, shugaban kungiyar masu noma, sarrafawa da kasuwancin dabino a Najeriya, ya ce hakan na faruwa ne saboda rashin kulawar gwamnatoci.
Yanzu Najeriya ta yunkuro domin ganin wannan batu ya zama tarihi, domin a jihar Sokoto kadai an samar da babbar gonar dabino wadda ita ce ta biyu mafi girma a Najeriya kuma yanzu haka gwamnatin jihar ta bayar da eka 300 na filin noma, kuma za a samar da eka 5,000 don habbaka noman dabinon.
Hukumar zakkah da wakafi ita ce ke hidima wajen bunkasa noman dabino, shugaban hukumar Muhammad Lawal Maidoki, ya ce matakin zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
An kaddamar da sashen itatuwan dabinon ne a wurin wani babban taron masu noma, sarrafawa da kasuwancin dabino na kasa, irinsa na farko da aka yi a Najeriya a jihar Sokoto.
Sarkin musulmi da gwamnan jihar Sokoto, a ta bakin kwamishinan kare muhalli Sagir Attahiru Bafarawa, sun jaddada goyon bayansu wajan bunkasa noman dabino. Hakazalika su ma ma'aikatun noma, kare muhalli da ciniki da masana'antu na tarayya, da kuma babban bankin Najeriya, da cibiyoyin gudanar da bincike-bincike sun jaddada aniyarsu wajen saka hannu ga habbaka harkar dabino a Najeriya.
Idan wannan shirin da aka assasa a Sokoto ya samu nasara ana sa ran nan da zuwa shekara ta 2024 zai rika samar da tan 100,000 a shekara kuma zai samar da aiki ga mutane 840,000 da kuma samar da kudin shiga naira biliyan 150.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir.
Your browser doesn’t support HTML5