Najeriya Na Neman Wani Dan Birtaniya Ruwa A Jallo Kan Yunkurin Kifar Da Gwamnatin Tinubu

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi a lokacin taron manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 02 ga watan Satumba, 2024 (Hoto: Facebook/Police)

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce za ta ba da tukwici mai tsoka ga duk wanda ya ba da bayanan da za su kai ga kama mutanen.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kaddamar da farautar wani dan asalin kasar Birtaniya da ke zaune a kasar wanda ta zarga da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A wani taron manema labarai da ya gabatar a Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Litinin, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi ya ce, mutumin mai suna Andrew Wynne wanda har ila yau ake kira Andrew Povich ya hada kai da wani dan Najeriya mai suna Lucky Ehis Obinyan wajen ta da husuma a kasar.

“Bisa bayanan sirri da muka tattara tare da hadin gwiwar takwarorin aikinmu, mun gano cewa wasu daga kasashen waje sun bayar kudade don a ta da husuma a Najeriya ta hanyar yin zanga-zanga da ba ta lumana ba.

“Andrew Wynne, ya kama haya a ginin Labour House inda ya bude wata makaranta domin batar da kama.

“Takardu da muka tattara da amsa laifi da wasu suka yi, sun nuna cewa Andrew Wynne ya yi ta ba da umarni, tare da bibiyar yadda zanga-zangar take gudana da fitar da kudade don a sauya zababbiyar gwamnati ta haramtacciyar hanya.

“Tuni an kama mutum 10 wadanda ke da hannu a wannan al’amari, kuma har an gurfanar da su a gaban kotu.” In ji Adejobi.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce za ta ba da tukwici mai tsoka ga duk wanda ya ba da bayanan da za su kai ga wadannan mutane.

Kakakin ya kara da cewa, tuni har shugaban ‘yan sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun ya sanar da hukumar ‘yan sanda ta kasa kasa kan farautar wadannan mutane.

A ranar 1 ga watan Agusta wasu 'yan Najeriya suka bazama akan tituna don yi zanga-zangar kan matsalar tsadar aryuwa da ta addabi kasar, zanga-zangar da ta jirkice ta koma tarzoma a wasu jihohin kasar.