Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Harin Da 'Yan Shi'a Su Ka Kai Wa 'Yan Sanda A Abuja Ya Hallaka Jami'an Tsaro 2


Rundunar 'yan sandan Najeriya
Rundunar 'yan sandan Najeriya

Wani hari da haramtacciyar kungiyar Shi'a ta Najeriya mai ra'ayin Iran ta kai a babban birnin tarayyar Abuja, ya yi sanadin mutuwar a kalla jami'an tsaro biyu, a cewar 'yan sanda, yayin da wasu uku kuma su ke cikin mawuyacin hali.

Sanarwar da mai Magana da yawun hukumar ‘yan sandan Abuja Josephine Adeh ta fitar, ta tabbatar da aukuwar farmakin da haramtaciyar kungiyar ta Harka Islamiyya ta Najeriya (ko IMN a takaice) ta kai wa jami’an tsaron ba tare da an takale ta ba.

A lokacin da aka kai harin a wani wurin da 'yan sanda ke duba ababen hawa, an kashe jami’ai 2 sannan wasu su 3 kuma an bar su rai kwakai mutu kwakai kuma an kai su asibiti, kazalika Adeh ta kara da cewa, sun bankawa motocin hukumar 3 wuta.

Rundunar yan sandan Najeriya
Rundunar yan sandan Najeriya

Kungiyar da ta samo tushen ta daga juyin juya halin Musuluncin da aka yi a Iran a shekararun alib 1970, wadda ake ayyana ta da IMN, har yanzu tana da alaka ta kut da kut da Iran.

An dade ana takun saka tsakaninta da hukumomin Najeriya wanda kuma aka aza mata takunkumi a shekarar 2019.

Maharan na ranar Lahadi sun kai harin ne dauke da adduna, wukake da kuma abubuwan fashewa, a cewar ‘yan sandan.

An kama mutane da dama kana kwamishinan ‘yan sandan Abuja, Benneth C. Igweh, ya yi Allah-wadai da mummunan harin inda ya lashi takobi cewa zai tabbatar da an gurfanar da wadanda suka kai harin.

'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)
'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)

Sanarwar 'yan sandan ta kara da cewa "A halin yanzu an shawo kan lamarin kuma an daidaita al'amura."

A watan Yulin 2021, bayan shafe fiye da shekaru biyar a gidan yari, wata kotu a Kaduna, a arewacin kasar ta saki shugaban IMN, Ibrahim Zakzaky da matarsa.

Zakzaky, wani malamin Shi'a ya sha kiraye-kirayen ga aiwatar salon Musulunci juyin juya hali irin na Iran a Najeriya - inda galibi al'ummar Musulmi mabiya Sunna ne.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG