Mambobin da shugabannin kungiyar ma'aikatan sun fara wannan yajin gargadi ne, domin matsawa gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjjejeniyar data kulla da kungiyar shekaru 10 da suka gabata.
Tun a shekara ta 2009 ne uwar kungiyoyin ta hannun kwamitin koli na hadin gwiwa, suka amince tare da rattaba hannu akan yarjejeniyar wadda ta kunshi batun samar da kudaden alawus, da samar da kayayyaki, da inganta muhallin aiki, kuma da batun daya shafi makarantun firamare dana sakandare na ‘yayan ma’aikatan jami’a.
Koda yake bayan shekaru, gwamnati ta fitar da kudaden alawsus din da tayi alkawari, amma ta danka su ga hannun kungiyar malaman jami’a ta ASSU, ita kuma nan take ta kwashe kashi 80, ta mika ragowar kashi 20 ga kungiyoyin ma’aikatan da ba sa koyarwa.
Amma masu sharhi akan lamuran ilimi a Najeriya na alakanta wannan takaddama da rashin jajircewa, da kuma yanayin rashin mutunta yarjejeniya daga bangaren gwamnati.
A ranar Juma’a mai zuwa ne wa’adin yajin aikin na gargadi zai kammala, kuma a hirar su da wakilin Muaryar Amurka, Komared Mohammed Jaji ya yi tsokaci game da mataki na gaba.
Rahotanni daga Jami’o’in mallakar gwamnati a sassan Najeriya na nuna cewa, mambobin kungogiyin ma’aikatan sun amsa kira ga umarnin kungiyoyin su.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5