Najeriya: Jam'iyyun Adawa Na Neman A Soke Zaben Shugaban Kasa

Sakamakon zabe

A ranar Litinin wasu daga cikin wakilan jam'iyyun na bangaren 'yan adawa suka fice daga zauren tattara sakamakon zaben bayan da suka nuna rashin gamsuwar kan abin da ke faruwa.

Jami’yyun PDP, LP da ADC, sun yi kira da a soke zaben shugaban kasar da aka yi, suna masu ikirarin an tafka magudi a zaben.

Shugabannin jam’iyyun sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka yi a Abuja a ranar Talata.

A cewar jam’iyyun, an hada baki da jami’an hukumar ta INEC a rumfunan zabe wajen yin arangizon kuri’u ta hanyar sakamakon zaben a na’urar IReV da ake ganin sakamakon a yanar gizo.

Shugaban jam’iyyar PDP Iyochia Ayu da na LP, Julius Abure sai na ADC Ralph Nwosu, su ne suka bayanna wannan matsaya yayin taron manema labaran a a Abuja.

Abure, shi ne ya yi magana a madadin jam’iyyun uku.

Jam’iyyun sun kuma ce sun yanke kauna ga shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu inda suka nemi da a nada wani wanda ba zai nuna son banbanci ba.

Shugabannin jam’iyyun sun yi zargin cewa rashin bayyana sakamakon zabe a akwatunan zabe ta shafin hukumar da aka tanadar don sanya sakamakon zabe wato IREV, shi ya tabbatar da cewa jami’an hukumar INEC sun sauya sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar ta Asabar.

“Ba a yi zabe da gaskiya ba balle ma a ce an yi adalci” sannan ya kara da cewa, ana ci gaba da soke sakamakon zabe a yankuna inda jam’iyyun adawa suke da rinjaye”. Abure ya ce.

A ranar Litinin wasu daga cikin wakilan jam'iyyun na bangaren 'yan adawa suka fice daga zauren tattara sakamakon zaben bayan da suka nuna rashin gamsuwar kan abin da ke faruwa.

Sai dai ciki watan sanarwa da ta fitar a ranar Talata, INEC ta musanta zargin da jam’iyyun suka yi, tana mai cewa kiran da suke yi a sauke Farfesa Yakubu ba shi da tushe balle makama.

Babban Sakataren yada labaran hukumar ta INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce akwai ka’idoji da hanyoyi da aka shimfida wajen shigar da korafe-korafe yana mai cewa zarge-zargen da suka yi, babu hujj a ciki.